Wasu fusatattun matasa sun dakawa abincin da É—an gidan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya je zai raba a jihar Gombe, kamar yadda ya ke a sauran jihohin Arewa da ya ke ta ziyar ta.
Wani faifen bidiyo, an ga matasan sun dirar wa motar dakon abincin, inda su ka riƙa diba suna yin nasu waje.
An hango matasan da suke kan motar na jefawa wadanda su ke kasa kunshin abincin da ya kun shi shinkafa, sukari, man girki da taliya.
Mota biyu aka baiwa Gombe kason ta na kayan abincin da su ka kunshi katan 3,500 na abincin, inda bayan an raba mota daya ba gare da hatsaniya ba, dayar kima sai matasan su ka daka mata wawa.