Mun janye shirin mu na hawan Bukukuwan Karamar Sallah don inganta zaman lafiya a Kano ~ Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero
Bayan turka-turkar kan Hawan sallah karshe dai Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, ya soke duk wasu shirye-shiryen hawan bikin karamar sallah.
Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke duk wasu shirye-shiryen gudanar da Bukukuwan Sallah karama a fadin jihar Kano.
Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a cikin wani dan takaitaccen faifan bidiyo a daren Larabar nan, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da shirin hawan.
Idan dai za a iya tunawa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da jami’an tsaro musamman rundunar yan sanda ta kasa shirinsa na gudanar da bukukuwan Sallah.
Aminu Ado ya bayyana a cikin faifan bidiyon cewa ya soke bikin ne saboda kokarin da wasu malaman addinin musulunci masu daraja da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya.
“Dole ne mu dakatar da shirin gudanar da wannan al’amari sakamakon shawarwari da malaman addinin Musulunci masu daraja da kuma dattawa suka bamu,” a cewar Aminu Bayero.
Dayawa al'ummar Kano sun shiga cikin firgici a lokacin da bangarori biyun suka bayyana shirye-shiryen su na Bukukuwan bikin Karamar Sallah, sai dai yanzu a iya cewa mazauna Kano musamman cikin birni zasuyi shagulgulan bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali