Shugaban Jami'iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas Sanusi ya yi kira da a tsagaita wutar siyasa zuwa bayan watan Ramadan.
Abdullahi Abbas ya yi wannan kira ne a lokacin da yake rabon kayan azumi a gidansa,
" Ina kira ga Yan siyasa da cewar mu dakatar da batutuwan Siyasa sai zuwa bayan a zumi" a cewar Abdullahi Abbas
"Yan siyasa da attajirai ku fito ku rabawa mabukata abincin da zasuci, ba dole sai irin abinda Abdullahi Abbas ya raba ba, zaku iya yin sama da nashi ko kasa da nashi" inji abdullahi abbas.