Na samu duk goyon bayan da nake bukata a masana'antar kannywood ~ Daraktan Film din Mai martaba, Prince Daniel (Aboki)
A baya-bayan nan, wasu labarai da aka wallafa sun ja hankalina da suka nuna cewa masana’antar Kannywood ta ki amincewa da ni saboda addini na, ita kuma Nollywood saboda ni dan Arewa ne.
Da farko dai ban yi hira da wata jarida ko kafar yada labarai ba dangane da wannan batu.
Amma duk da haka bari na dan yi Karin haske. Na halarci wani taron masana’antar Nollywood da Hollywood a birnin Los Angeles na jihar California dake kasar Amurka a farkon wannan watan, inda a sashen tambaya da amsa na taron aka tambaye ni Æ™alubalen da muka fuskanta lokacin yin Film din Mai Martaba da gwagwarmayar kaiwa matakin kambun fina-finai na duniya na Oscars.
Na ambaci batutuwa da dama irin su fargabar matsalar rashin tsaro yayin yin Film tare da ma'aikata masu yawa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da matsalolin kudi wanda babu wanda yake son yin kasadar amincewa su bamu kudinsu, la'akari da cewa ni sabon darakta ne wanda ke aiki tare da rukunin sababbin jarumai.
A wani lokacin bangaren masana’antar Kannywood na yi mana kallon ‘yan Nollywood, su ma Nollywood suna kallonmu a matsayin 'yan Kannywood, saboda kawai ni dan Arewa ne.
Na yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya domin taimaka wa masu sauraro a cikin zauren su fahimci ɓangarorin masana'antar Fina-finai a Najeriya da kuma yadda yake da ƙalubale a gare mu a lokacin.
Na yi amanna an yiwa wannan bayanai nawa gurguwar fahimta.
Domin fayyace zahiri, masana’antar Kannywood ba ta taba nuna min kiyayya ba ta kabilanci ko addini.
Hasalima, masanba’antar itace babban ginshiÆ™in goyon bayan da na samu a matsayina na mai shirya fim.
An nuna min kauna a fili ta hanyar babban goyon bayan da muka samu daga masu kallo da sauran al-umma a lokacin da muka nuna fina-finan mu a gidajen kallo, da kuma karfafawa daga kwararrun ‘yan masana’antar tsofaffi da sababbin shiga.
A yau ina alfahari, ni dan Film ne a Najeriya, wanda na fito daga arewa. Ina zaune a jihar Kano, inda nake gudanar da sana’ar tawa, daga Kannywood.
Na samu goyon baya mai yawa, ba tare da nuna bambanci ba.
Saboda haka na tsaya tsayin daka wajen hada kai da takwarorina da wadanda suka kafa masana’antar Kannywood domin daukaka martabar masana’antarmu da bayar da labaranmu ga duniya da samar da guraben aikin yi ga matasanmu, tare da fito da zahirin halin da muke ciki sabanin labaran da ake bayarwa akan Arewa da ke nuna rikici da matsalolin rashin tsaro.
Prince Daniel (ABOKI)
Babban daraktan shirin, Mai Martaba