Naira ta fadi da kashi 0.43
A jiya Litinin, darajar Naira ta fadi a kasuwannin kasar, inda aka yi hada-hadar ta kan N1,498.98 akan Dala.
Bayanai daga babban bankin Najeriya CBN sun nuna cewa Naira ta yi asarar N6.49.
Wannan ya nuna raguwar kashi 0.43 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da Naira ta rufe a kan N1,492.49 zuwa dala.
Asarar ta biyo bayan É—aguwar darajar Naira kwanaki uku a makon da ya gabata.
Duk da haka, Naira ta É—an yi rawar gani idan aka kwatanta da dalar Amurka saboda sauye-sauyen da CBN ya yi na inganta kasuwar musayar kasashen waje, FX.
Manazarta na ci gaba da yaba wa CBN saboda ci gaban da kudin gida ke samu tun watan Disambar 2024.