Rikicin masarautar Kano Sheikh Lawan Triumph ya yi kira ga tsagin Sarki Aminu Ado Bayero da ya hakuri da Hawan bikin Karamar sallah
Babban malami a Kano, Limamin masallacin Juma'a na Triumph dake Kano, Malami ne wanda ke takun sake da Gwamnatin Kano Sheikh Lawan Triumph ya yi wannan kira a lokacin da yake gabatar da Tafseer na Ramadan.
"Muna Kira da Alh. Aminu Ado Bayero ya yi hakuri karya fito hawan sallah, Inji sheikh Abubakar lawan triumph
Daman duniya ta sheda shi sarki Aminu ado mutum ne mai hakuri, yakamata ya nuna hakurin sa anan Saboda kare rayukan Al-ummar jihar Kano. A cewar Malam Triumph.
Mahaifinka Marigayi Sarkin Kano Alh. Ado Bayero Allah ya yi masa gafara mutum ne wanda duniya ta shaide shi da hakuri kamar yadda kaima aka shaideka,
Bashida abokin rigima kamar yadda kaima kasami shaida, mutum ne mai san zaman lafiya kamar yadda kaima ake maka shaida,
Sabida San zaman lafiya na marigayi sarki Alh. Ado Bayero yana sanyawa ana addu'oin zaman lafiya a wannan jiha.
Kayi hakuri Alh. Aminu Ado Bayero kayi koyi da mahaifinka, kayi hakuri ka janye kudirinka na Hawan Sallah, kabarwa Malam Sanusi Lamido Sanusi ya je ya yi hawan sa.
Tunda shine wanda Maigirma Gwamna ya ayya a matsayin wanda zaiyi hawan sallah, daga bisani kaima ka karbi izini daga bangarorin hukumomin tsaro kuma suka amince maka.
Bamu da inda yafi Kano, kada sanadiyyar ka ya zamana anzubar da jini, anyi asarar rayuka a Jihar mu mai albarka. A cewar Malam Lawan Triumph.
Sabon Kwamishinan yan sandan jihar Kano, dai yace ya shirya tsaf don gannin ya bada tsaro, yadda yakamata a wajen gudanar da bikin hawan sallah a bana.