Rundunar ƴansanda ta jihar Kano ta hana hawan sallah a lokacin bukukuwan Ƙaramar Sallah saboda dalilan tsaro da kuma bukatar tabbatar da zaman lafiya.
Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai a yau Juma’a.
CP Bakori ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin bukukuwan.
A cewarsa, bayanan sirri da aka samu sun nuna akwai barazana ta tashin hankali da ke tattare da hawan, wanda zai iya haifar da tarzoma.
“Bayan sahihin rahotannin sirri na tsare-tsare da ’yan bata-gari da masu daukar nauyinsu suka shirya na amfani da bawan sallah wajen kawo tarnaki, rundunar ‘yan sandan tare da tuntubar gwamnatin jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke shawarar haramta duk wani abu na hawa a fadin jihar,” in ji CP Bakori.