Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na ƙasa, INEC, a matsayin mai bashi shawara kan harkokin dabbobi.
A wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya sanar da nadin a jiya Juma'a.
Sanarwar ta ce, Tinubu ya hori Jefa da ya yi amfani da kwarewar da wajen kawo ci gaba a harkar ta dabbobi a kasar.