Wasu Mazauna Kududdufawa Fegin kara, da garin iya dake Jihar Kano, na neman daukin mahukunta bisa yadda ake kona Kashi a yankin.
Al’ummar garuruwan kudiddifawa Fegin kara da Garin iya, na neman daukin mahukunta saka makon yadda wasu mutane ke amfani da filaye wajan kona Kashin mutane domin amfaninsu.
Al'ummar sun bayyana cewa Koda bacci basayi Idan an Kunna wutar.
Guda daga cikin mazauna yankin Bashir Nasir yace Akwai bukatar mahukunta dasu bibiyi lamarin domin tallafawa al'ummar yankin duba yadda suka kwashe tsahon lokacin suna kokawa kan halin da suke ciki
Saidai koda wakilin mu ya ziyarci wajan ya zanta da shugaban masu wannan kona kashin Baba Gambo wanda yace suna kokarin ganin an daina cutar da al'ummar.