Yan Bindiga sunyi awon gaba da wani matashi a Jihar Kano
Yan bindiga sun kai hari tare da sace wani matashi a garin Zakirai dake karamar hukumar Gabasawa a nan Kano.
Yayin wannan hari yan bindigar sun yi garkuwa da wani matashi Mohammed Bello, É—an shekara 20, sannan wani mai suna Abubakar ya ji rauni.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kai hari gidan wani mutun mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda ma’aikaci ne a wani asibiti mai zaman kansa a garin na Zakirai.
Kakakin rundunar Æ´an sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an Æ´an sanda sun fara neman maharan, Kuma kokarin ceto wanda suka yi garkuwa da shi.