Majalisar wakilai ta bukaci Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da ta umarci kamfanunuwan sadarwa na intanet a Æ™asar da su toshe dukkan shafukan yanar gizo da ke dauke da “abin da bai dace ba da kuma hotuna ko bidiyoyin batsa” ba tare da wani jinkiri ba.
An amince da wannan kuduri a ranar Talata bayan wani kudiri da Dan majalisa Dalhatu Tafoki daga Jihar Katsina ya dauki nauyi.