A yau Juma’a ne Rarara Zai Angwance da A’isha Humaira.
A Cikin daren ranar Alhamis ne hotunan shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara tare da abokiyar aikinsa A’isha Humaira suka fara yawo a kafafen sada zumunta, da ke nuna Mawaƙi Rarara zai angwance a wannan rana ta Juma’a.
Majiyar Kano time ta ruwaito cewa, za'a ɗaura auren shahararren mawaki a Nijeriya Dauda Kahutu Rarara tare da abokiyar aikinsa A’isha Humaira a yau Juma’a, a garin Maiduguri da ke jihar Borno.
Idan zaku iya tunawa dai Dauda Rarara da Aisha Humaira sun dauki lokaci suna jan zaren su na soyayya, wanda zuwa yanzu ake gannin tarayyar tasu tayi karshe mai kyau. Indai har aka samu damar gudanar da wannan Aure.