A wannan rana Ubangiji ya dauki ran Jarumin masana'antar Kannywood Rasuwa Baba Hasin,
An yi Jana'izarsa kamar addini Muslunci ya tanada, da misalin karfe 04:00 na yammacin wannan rana, a gidansa dake Rafin Kuka a karamar hukumar Kumbotso.
Kafin rsuwarsa ya kasance Jarumi wanda ke taka rawar mahaifi a cikin Fina-finan da ya yi,
Ya rasu yabar 'ya'ya da dama daga cikin su akwai Basma wacce take itama tana fitowa a cikin Fina-finan hausa a matsayin 'Ya.
Ubangiji ya jikansa yasa Aljannar firdausi ce makoma.