An sauyawa AIG Usaini Gumel wurin aikin bayan daya bayyana ra’ayinsa kan sanya dokar ta baci a jahar Ribas.
Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, ya mayar da Usaini Gumel Mataimakinsa da ke kula da Yankin Zone 7 Abuja zuwa Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare,
Bisa zargin cewa ya bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da Gwamna Sim Fubara a matsayin abin da ya saɓawa kundin tsarin mulki.
An rawaito cewa Gumel ya faɗi ra’ayinsa kan dokar ta-ɓaci ne a cikin ofishinsa yayin wata tattaunawa da wasu daga cikin abokan aikinsa, amma ɗaya daga cikinsu ya tona masa asiri ya kai rahoto ga babban Sufeto Janar.
Zone 7, wacce ke kula da Babban Birnin Tarayya da Jihar Neja, ke da matakin aiki mai muhimmanci da kuma ɗaukaka, ana kallon Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare a matsayin wuri na ladabtarwa.