An shiga fargaba a APC kan batun dawowar Kwankwaso jam'iyyar
A yayin da a ke ci gaba da rade-radin yiwuwar sauya shekar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC, wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan yunkuri na tsohon gwamnan jihar Kano ya haifar da fargaba a cikin jam’iyyar.
Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana wa jaridar TRIBUNE cewa wannan yunkuri da ake cewa ya samo asali ne daga yarjejeniya tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da jagoran na NNPP, na janyo rashin jin dadi a bangaren shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanata Barau Jibrin, da ke neman tikitin takarar gwamnan Kano a 2027.
Majiyoyin jam’iyyar sun ce, idan babu wani tangarda, ana sa ran Kwankwaso zai gana da Shugaba Tinubu bayan ya dawo daga tafiyarsa zuwa Faransa da Birtaniya.
Baya ga Kwankwaso, wasu Æ´an majalisar tarayya uku na NNPP sun gana da shugaban jam’iyyar APC ta kasa a makon da ya gabata kafin sanar da sauya shekar su zuwa jam’iyyar mai mulki.
Duk da cewa sakatariyar kasa ta NNPP da reshen Kano suna ci gaba da musanta rade-radin sauya shekar Kwankwaso, shugaban jam’iyyar APC na kasa da na jihar Kano sun tabbatar da yunkurin a maganganunsu cikin makon da ya gabata.
Bincike ya nuna cewa yayin da Tinubu ke kokarin samun goyon bayan Kwankwaso da magoya bayansa domin zaben 2027 saboda tasirinsa a Kano, wasu jiga-jigan APC na fargabar cewa hidimar da suka yi za ta tashi a banza a yarjejeniyar da Kwankwaso da NNPP.
Wani jigo daga jam’iyyar ya shaidawa Nigerian Tribune cewa shugaban APC na Kano yana samun karfin guiwa daga wasu masu ruwa da tsaki a Abuja da ka iya rasa komai sakamakon kusancin da ake samu tsakanin shugaban kasa da Kwankwaso da ‘yan majalisar NNPP.
Majiyar ta kara da cewa an sha alwashin bai wa ‘yan majalisar NNPP da ke shirin sauya sheka tikiti kai tsaye domin dawowa majalisar tarayya.
“In har Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yanke shawarar bin Kwankwaso, hakan na nufin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, zai yi watsi da burin zama gwamna,” in ji majiyar.
Sai dai a wata hira ta wayar tarho da Nigerian Tribune, Ladipo Johnson, wanda ya tabbatar da yiwuwar sauya shekar Kwankwaso, ya bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa har yanzu na tuntubar masu ruwa da tsaki ne.