Ana zargin Mataimakin Gwamnan Bauchi da kwadawa Ministan harkokin waje mari
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, a wajen nadin sarautar tsohon gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abdullahi Abubukar a matsayin Makaman Bauchi.
Hakan ya biyo bayan cacar baki tsakanin gwamnan Bauchi Bala Muhammad da ministan harkokin waje Maitama Tuggar, wanda ya fusata mataimakin gwamnan tare da zabgawa ministan mari.
Sai dai mataimakin gwamnan na Bauchi, Auwal Muhammad Jatau, ya musanta labarin marin ministan.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Muslim Lawal, ya fitar, mataimakin gwamnan ya ce ta yaya mataimakin gwamna zai daki minista?
Ya ce ba ya taba ganin hakan zai iya faruwa a Bauchi kuma wannan shi ne karon farko da ya ke jin hakan.
Sai dai duk kokarin da aka yi domin jin ta bakin ministan harkokin wajen, Yusuf Tuggar, bai samu ba har zuwa wannan lokaci.