Rundunar ƴansandan jihar Kano ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa wa umarnin da ƴansandan suka bayar na haramta Hawan Sallah a Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta jaddada matsayinta na haramta Hawan Salla a faɗin jihar, kuma duk wanda aka samu da laifin saɓa umarnin zai ɗanɗana kuɗarsa.
Kwanaki kafin ranar Sallah ne dai rundunar ƴansandan jihar ta fitar da sanarwar haramta Hawan Sallah a Kano bayan da ta ce ta samu bayanan sirri na wasu ɓata-gari da ke da aniyar haifar da tashin hankali a lokacin hawan.
Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya kafa wani kwamitin ƴansanda mai mambobi takwas domin gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka samu a ranar Sallah lokacin da tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ke komawa gida bayan jagorantar Sallar Idi.
A lokacin da aka samu hatsaniyar dai an kashe wani jami'in sintiri tare da raunata wani da ke aikin bayar da tsaro ga tawagar sarkin Kano Mal Sanusi Lamido Sanusi.