Ƙarancin ruwa: Gwamnan Kano ya bamu umarnin kai ɗauki a Ƙaramar Hukumar Warawa ~ Kwamishinan muhalli
Dakta Dahir M. Hashim, Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, ya baiyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu rahoto kan matsanancin ƙarancin ruwa a garuruwan Talawa, Ba'awa da Dinyari a ƙaramar hukumar Warawa, ya bada umarnin a kai musu ɗauki don shawo kan lamarin.
A cewar Kwamishinan, tuni ya kai ziyarar gani-da-ido domin duba halin da ake ciki tare da fara aikin samar da ruwan sha a garuruwan.
Hashim ya kuma baiyana cewa a halin yanzu, gwamnatin jihar ta gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana fiye da 120 a sassa daban-daban, ciki har da garin Falgore, Zangon Ranka, Sata, Hayyin tagidadu, Kafin Agur, Kyallin Bula, Mariri da sauran su.
"Ina tabbatarwa da jama'ar Jihar Kano cewa Ma’aikatar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano tana ɗaukar matakai masu ɗorewa don tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha ga al’umma.
"Ina ƙara jaddada bukatar al’umma da su kula da wadannan rijiyoyi da aka samar, domin tsaftataccen ruwa yana hana cututtuka, yana karfafa halartar makaranta ga yara, sannan yana rage cin zarafin da ake yi wa mata da yara kanana a yayin da suke yawo neman ruwa," a cewar sa.
Ya kuma yi bayanin cewa sauyin yanayi da tsananin zafin rana ne ke haddasa ƙafewar rafuka da rijiyoyi, wanda ke jefa al’umma musamman na karkara cikin matsanancin halin rashin ruwan sha.