Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, a ranar Juma'a, ya kai ziyara wadda ya bayyana a matsayin ziyarar bayan Sallah ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa dake Kaduna.
Jagoran ‘yan adawa din ya samu rakiyar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon gwamnan Jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam; tsohon gwamnan Jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, da tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da wasu da dama.
Atiku, wanda ya wallafa labarin ziyarar a shafinsa na sada zumunta da aka tantance, ya bayyana ganawar da Buhari a matsayin “lokaci mai ban sha’awa.”