CBN ya musanta samar da Sabbin Takardun Kudin N5,000 da N10,000
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karyata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta kan fitar da sabbin takardun kudi na Naira dubu biyar (N5,000) da dubu goma (N10,000)
Cikin wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafinsa na X na ranar Laraba, ya bayyana cewa labarin babu gaskiya a cikinsa kuma ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da shi.
Sanarwar ta ce: “Wannan bayani ba daga CBN yake ba, domin kuwa ya kamata mutane su sani cewa sahihin shafin hukumar shine cbn.gov.ng, wanda kuma ta nan ake samun bayanai daga gare mu.”
Haka kuma, babban bankin ya musanta zargin cewa wani mataimakin gwamna mai suna Ibrahim Tahir Jr ne ya fitar da labarin. Ya ce babu irin wannan mutum a cikin bankin, kuma yanzu haka ana bincike don gano tushen jita-jitar.
A baya-bayan nan, an hango wata sanarwa a kafafen sada zumunta da ke dauke da hotunan sabbin takardun kudi, inda aka nuna Naira dubu biyar da hoton Chief Obafemi Awolowo, da Naira dubu goma da hoton Dakta Nnamdi Azikiwe. Wannan jita-jita na nuni da cewa sabbin takardun an kirkire su ne don girmama manyan shugabannin da suka taka rawa wajen ci gaban Najeriya.
Sai dai CBN ya jaddada cewa babu wani shiri na fitar da sabbin takardun kudi, inda ya bukaci al’umma su dogara da ingantattun majiyoyi wajen samun sahihan bayanai.
CBN ya jaddada cewa babu wani shiri na fitar da sabbin takardun kudi, inda ya bukaci al’umma su dogara da ingantattun majiyoyi wajen samun sahihan bayanai.