Dangote ya sake rage farashin sari na man fetur. Matatar man dangote ta sake rage farashin sari daga defo na man fetur zuwa N865 kowace lita.
Kamfanin ya sanar da abokan cinikinsa game da rage farashin a sanarwar da ya fitar a yau Alhamis.
Sabon farashin dai shi ne na ragin Naira 15 daga Naira 880 kan kowace lita da matatar ta sayar a jiya Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta ce za a ci gaba da sayar da danyen mai da tataccen mai a naira Mai makon Dalar Amurka a kasar.