Shugaba Bola Tinubu ya gana da Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, a birnin London a makon da ya gabata, kamar yadda rahoton Africa Report, wanda TheCable ta naƙalto, ya bayyana.
A cewar rahoton, wasu hadiman shugaban kasa guda biyu da ba a bayyana sunayensu ba sun tabbatar da cewa ganawar ta faru.
Rahotanni sun ce ganawar da Fubara ta gudana ne bisa bukatarsa, domin yana da sha’awar dawowa kujerar gwamna.
A yayin tattaunawarsu, Fubara ya yi alkawarin yin wasu gyare-gyare don warware rikicin siyasar da ke gudana a jihar Rivers.
Wasu hadimai da suka san da tattaunawar sun ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa, kuma akwai yiyuwar a janye dokar ta-baci kafin wa’adin watanni shidan da Tinubu ya É—auka ya cika.
A ranar 18 ga Maris, Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Rivers, yana mai bayyana rikicin siyasa da ya dade yana faruwa a jihar.
Shugaban kasar ya dakatar da Fubara daga kujerar gwamna, tare da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin majalisar dokokin jihar, na tsawon watanni shida.
Tinubu ya nada Ibok-Ete Ibas, tsohon mataimakin hafsan sojin ruwa, a matsayin mai kula da jihar guda daya tilo.