Fitaccen malamin addinin musulunci Dr. Idris Abdul-Aziz Dutsen Tanshi ya rasu.
Cikin wani sako da Dr. Ibrahim Disina babban malami a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Facebook ya tabbatar da rasuwar tasa.
Inda yace”Mutuwa Rigar kowa Allah ka jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, Allah ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakuransa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana ameen”