Guda daga cikin masu shirya fina-finan a masana'antar kannywood Umar Jalo, yana bukatar neman dauki sakamakon cutar shanyewar barin jiki
Cikin wani bidiyo da guda daga cikin jaruman masana'antar shirya fina-finan na masana'antar kannywood, Jamilan Ibro ta wallafa ta bayyana inda guda daga cikin wanda ya bawa masana'antar gudunmawa a lokacin da taurarunsa yake haska, Malam Umar Jalo yana cikin wani yanayi wanda yake bukatar neman dauki.
Jamila ya wallafa wannan bidiyo tana mai bayyana cewar, Jalo yana da mata Biyu ga yara, wanda zuwa yanzu baya iya fita yana zaune a cikin gida, ga kuma yadda rayuwa tayi tsada.
"Daraktan Jarumin Finafinan Hausa, Umar Yakubu Jalo na fama da matsanancin rashin lafiya, Inda ya samu shanyewar barin jiki kuma ba iya magana" a cewar ta.
Tana cikin wannan bidiyo ne tafashe da kuka da ita da Umar Jalo, wanda duk wanda ya kalli wannan bidiyo zai tausaya masa.
Hakan yasa tayi kira ga 'yan masana'antar kannywood dasu kaiwa Umar Jalo agajin gaggawa, dama wanda Allah ya horewa.
Irin makamancin wannan bidiyo bawai anfara sanya shi akan Umar Jalo ba, anyi na wasu jarumai kamar Marigayya ladidi, marigayi karkuzu, Halisa Muhammad da dai sauransu.
Abun tambaya anan shine ko shin meyasa wannan masana'anta bata bibiyar tsafaffin jarumai, masu shiryawa, masu bada umarni da dai sauransu,
Wanda har sai ansanya su a kakafen sada zumunta ko kafafen yada labarai? A ina matsalar take? Yaushe ne zasu gyara?