Gwamnan Jihar Kano Ya Biya Ragowar Kuɗin Makaranta Na Ɗaliban Da Suka Kammala Karatun Lafiya A Ƙasar Cyprus
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya biya ragowar kuɗaɗen makaranta na ɗaliban Jihar Kano mutum 84 da ke karatun lafiya a Jami’ar (Near East University) ta ƙasar Cyprus.
Ɗaliban waɗanda suka kammala karatunsu tun a shekarar 2016 gwamnatin da ta gabata ta kasa biya musu ragowar kuɗaɗen makarantar da ake bin su, yanzu haka gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya musu kuɗin wanda ya kai Naira Biliyan 2.5.
Bayan biyan kuɗin a yanzu, tuni makarantar ta shiga shirye-shiryen ba wa ɗaliban takardunsu na shaidar kammala karatun ta hannun hukumar ba da tallafin karatu ta Jiha ta ƙarƙashin jakadan Najeriya da ke Turkiyya.