Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu dokoki guda hudu da suka kafa sabbin hukumomi da aka tsara domin karfafa tsarin hukumomi da kuma kara kaimi mai dorewa a fadin jihar.
Sabbin dokokin da aka sanya wa hannu sun tanadi kafa hukumomi kamar haka:
1. Hukumar bayar da kariya ga al' umma
2.
Hukumar kulawa da Tallace tallace ta jihar kano .
3. Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano.
4. Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Jihar Kano.
Ana sa ran wadannan dokoki wadanda a halin yanzu suke cikin tsarin dokokin jihar Kano, za su zaburar da kirkire-kirkire, da tallafa wa kananan ‘yan kasuwa, da tsara yaddda zaa gudanar da tallace-tallace, da inganta kariya da kuma hidimtawa alumma
Gwamna Yusuf ya bayyana rattaba hannun a matsayin wani gagarumin mataki na tabbatar da manufofin gwamnatinsa na samar da Kano ta zamani, mai hade da tattalin arziki.
Ya jaddada cewa sabbin hukumomin za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo jari, da aiwatar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Ya kuma yi gargadin cewa karya dokokin wadannan dokoki za'a fuskanci hukunci mai tsauri, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da bin doka da oda.