Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Juma’a, 18 ga Afrilu da Litinin, 21 ga Afrilu, a matsayin ranakun hutu don bikin Good Friday da Easter Monday.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.
A cikin sanarwar, Dr. Tunji-Ojo ya taya daukacin Kiristoci murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka na Ista, yana mai yi musu fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali.