Hajjin Bana: An Sanya Ranar da Alhazan Kano Zasu Fara Tashi Zuwa Saudiyya
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce Maniyatan jihar za su Fara tashi zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali a bana a ranar 13 ga watan mayun shekara ta 2025.
Shugaban Hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan a yau yayin wata ziyara da ya kai cibiyoyin karatun koyon Aikin Hajj na kananan hukumomin Ungogo da Bichi, a wani bangare na shirin Hajjin shekarar 2025.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikowa Jaridar Raihana ranar asabar.
Sanarwar ta ce Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa, bisa ga jadawalin da Hukumar kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, cewa Jihar Kano za ta fara jigilar alhazanta zuwa Saudiyya tare da kamfanin jirgin sama na Max Air a ranar 13 ga Mayu, 2025.
Ya kara da cewa Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata tun da wuri, domin tabbatar da cewa an gudanar da jigilar alhazan cikin nasara da tsari.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya ja hankalin mahajjata masu niyyar tafiya da su rika halartar karatun koyon Aikin Hajji a kai a kai domin amfanin kansu.
Haka kuma, ya gargade su da su kiyaye bin dokoki da ka’idojin na hukumomin Najeriya dana wadanda Saudiyya suka shimfiÉ—a domin tafiyar da aikin Hajji.
Shugaban Hukumar tare da dukkan mambobin kwamitin da daraktoci sun halarci wannan ziyarar.