Hisbah a Kano za ta fara kamen masu Zance a cikin mota
Hukumar dake hani da mummunan aiki, da umarni da kyakkyawan aiki Hisbah a jihar Kano, ta sha alwashin sanya kafar wando daya da masu yin zance a mota.
Mataimakin Babban kwamandan hukumar Dr. Mujahiddeen Aminuddeen ya shaidawa Jaridar Raihana, cewa suna yawan samun korafi kan yadda samari da 'yan matan ke yin lalata a cikin mota, da sunan zance.
A cewar sa hakan ne ya sanya hukumar ta shirya daukan mataki don magance wannan matsala a cikin birnin Kano da kewayen ta.
Wanda a karshe ya yi kira ga iyaye wajen sanya ido akan 'ya'yan su, da Jan kunnen masu aikata haka domin hukumar su zatayi aiki babu sanni babu sabo.