Hukumar Kula da Zirgar-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta gargaɗi direbobin da ke kai wa jami’anta farmaki yayin gudanar da ayyukansu akan tituna.
Shugaban Hukumar, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya yi wannan gargaɗin a cikin sanarwa da Kakakin Hukumar, Abubakar Ibrahim Sharaɗa ya aike wa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba, 9 ga watan Afrilun 2025.
Sanarwar na zuwa ne bayan wani farmaki da wasu mutane cikin baburin Adai-daita Sahu suka kai wa jami’an na KAROTA yayin da suke tsaka da aikinsu a kan hanyar zuwa Gidan Zoo .