Kwamitin da Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano Abba El-mustapha ya kafa, karkashin jagorancin Daraktan Dab'i Abubakar Zakari Garun Babba, domin aikin saka ido kan yadda gidajen wasanni a Jihar Kano za su gudanar da shaguggulan bikin sallah, ya sami wani dandalin wasa da ke cikin gidan ZOO da laifin rashin da'a ta hanyar yin rawa mace da namiji a wani salo na fito na fito da doka tare da fatali da kunya irin ta malam Bahaushe.
Wannan na kunshe ne ta hannun jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar Abdullahi Sani Sulaiman daya rabawa manema labarai,
Inda yace tunda farko Hukumar Hisbah ce ta sanarwa da jami'an Hukumar tace fina-finai halin da ake ciki a wannan dandalin wasa, ta hanyar jami'an mu na farin kaya da ke gudanar da aiki cikin gidan ZOO domin tabbatar da doka da oda tare da yaki da rashin da'a.
Bayan tabbatar da hakan Hukumar tayi awon gaba da kayan da ake gudanar da wasa a gurin, inda a yanzu haka wacce ake zargi da aikata wannan rawa ta rashin da'a ke tsare a hannun jami'an Hisbah, sai dai tuni abokin rawar nata ya gudu, an kuma baza jami'ai wajen nemo shi, duk inda ya shiga.
Shugaban Hukumar tace fina-finai Abba El-mustapha ya godewa al'ummar Jihar Kano, tare da jami'an Hukumar Hisbah da 'Yan sanda tare da jami'an tsaron farin kaya na DSS, dangane da taimakonsa a koda yaushe wanda shine silar dukkannin nasarar Hukumar kawo ya wannan lokaci.