JAMB Ta Sanar da Ranar Fara Jarrabawar 2025
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Najeriya (JAMB) ta bayyana cewa za a fara jarabawar wannan shekara daga ranar 25 ga Afrilu, 2025.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, an bayyana cewa za a fara jarrabawar gwaji ta JAMB-Mock a ranar 10 ga Afrilu.
Haka kuma, hukumar ta bukaci dalibai su fitar da katunan jarrabawar su daga ranar 3 ga Afrilu domin samun cikakkun bayanai kan ranar, lokacin, da wurin da za su yi jarrabawar.
masu shirin rubuta jarrabawar da su shirya yadda ya kamata don gujewa matsaloli a ranar jarabawa.