Jihohi 30 za su fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani, in ji gwamnatin taraiya
Hukumar Kula da Kogi da Tafki ta Ƙasa (NIHSA) ta bayyana cewa al’ummomi 1,249 a cikin jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja na cikin haÉ—arin ambaliyar ruwa mai tsanani.
Hukumar ta Æ™ara da cewa al’ummomi 2,187 da ke cikin Æ™ananan hukumomi 293 su ma suna cikin jihohin da ke fuskantar haÉ—arin ambaliya a matsakaicin mataki.
Da yake magana a Abuja ranar Alhamis yayin Æ™addamar da hasashen ambaliya na shekara ta 2025, Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Joseph Utsev, ya ce ambaliya na É—aya daga cikin manyan bala’o’in da ake fama da su a Najeriya, kuma sauyin yanayi yana Æ™ara tsananta faruwar ta.
Utsev ya bayyana cewa jihohin Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Rivers da Jigawa na daga cikin muhimman wuraren da ake sa ran za su fuskanci ambaliya mai tsanani.
Ya ce hukumar ta kuma ƙaddamar da wani sabon shiri na hasashen ambaliya da ke mayar da hankali kan kowane yanki da ƙauyuka daban-daban a faɗin ƙasa.