Kansila mai ci a Mazabar Kofar Mazogal dake birnin Kano ya rasu
Alhaji Shehu Babba Alhassan, mai wakiltar mazaɓar Kofar Mazugala a karamar hukumar Dala ta Jihar Kano, ya rasu yana da shekaru 55 a duniya, ya rasu ya bar mace 1, da yara 5 kamar yadda rahoton Grassroots Parrot ya tabbatar.
Wata majiya daga cikin iyalansa ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon fama da cutar daji (cancer) a ranar Laraba, a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano.