Mai shari’a S.M Shuaibu na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yankewa wani mai sana'ar kwalliya, Abdullahi Musa Huseini (wanda aka fi sani da Amuscap) hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa laifin wulakanta Naira.
An daure shi ne bayan ya amsa laifi guda daya da ya shafi cin zarafi da lalata naira.
Da aka gurfanar da shi a gaban kotu, Huseini ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda hakan ya sa lauya mai shigar da kara, Zarami Mohammed, ya gabatar da bayanin lamarin da kuma hujjoji masu gamsarwa a gaban kotun.
Da ya ke yanke hukunci, Mai shari’a Shuaibu ya same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
An kama wanda ake tuhuman ne biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu kan sa hannun sa wajen wulakanta kudin Najeriya da gangan ta hanyar yin liƙi a wajen bikin aurensa.
Bincike ya nuna cewa da gan-gan Huseini ya tozarta kudaden Naira tare da yin amfani da shi wajen yin katsalandan da gargadi da kuma yakin neman zaben da hukumar EFCC ke yi.