Kotu Ta Tura Mawaƙi Alhaji Surajo Mai Asharalle Zuwa Gidan Yari
Wata Kotu ta tura fitaccen mawaƙin Asharalle a jihar Katsina Alhaji Surajo Mai Asharalle zuwa gidan gyaran hali har ya zuwa lokacin da za a cigaba da shari'a akan zargin da ake masa na harbin wasu jami'an hukumar Hisba a jihar Katsina.
Wata majiya ta rawaiyo cewar, lauya mai kare Alhaji Surajo mai Asharalle ya ce kotu ta dage shari'ar zuwa ranar Alhamis 10 ga Aprilu 2025 domin ci gaba da sauraren kara.
An dai zargi Alhaji Surajo mai Asharalle da ya'yansa 5 yin harbi a lokacin rikicinsu da Hukumar Hisba a gidansa dake ƙofar Ƙaura a jihar Katsina.