Kwamandan rundunar tsaron mafarauta dake kula da dazuka ta kasa reshen Kano ya ja hankalin mafarauta da surunga kasancewa da katin shaidarsu na farauta a duk In suka tsinci kansu
Babban kwamandan rundunar tsaro ta mafarauta dake kula da dazuka ta kasa reshen jihar kano, (Nigerian hunters and forest security service) Abdullahi Al-amin yayi Allah wadai tare bayyana Alhinin sa bisa abunda ya faru ga Mafarautan Kano a Jihar Edo.
Inda ya ja hankalin duk wani mafarauci ya kasance yana tare da katin shaidar sa na mafarauta (I.D. CARD) a duk inda ya tsinci kansa.
Kwamandan yace shirye shirye sunyi nisa, domin sun kusa kammala hada takardun da zasu mikawa Fadar Shugaban kasa da Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa da kuma ragowar hukumomin da lamarin ya shafa Kai tsaye.
Yace ba zasu bari ana yiwa 'yan uwan su mafarauta irin wannan cin kashin ba, hatta Gwamnan Jihar Edo sai sunkai masa takarda duk da sun gana da Gwamnan Jihar kano akan lamarin, domin iyalan mamatan suna cikin wani hali wanda sai an tausaya musu.
Daga nan yayi fatan Al'ummar kano za su Cigaba da gudanar da bikin Sallah karama Cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali tare da bin doka da oda.