A yau Alhamis ne wani kwamiti mai karfi wanda gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa, karkashin jagorancin mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya tafi jihar Edo domin gudanar da bincike kan kisqn mafarauta 16 da aka yi a kauyen Uromi na jihar.
Wannan mummunan lamari da ya faru a watan da ya gabata, ya haifar da tashin hankali a cikin al’ummar da abin ya shafa.
A cewar babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shu’aibu, an É—orawa kwamitin alhakin aikin gano musabbabin kisan don daukar matakan da su ka da ce da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Kwamitin ya hada da manyan mutane irin su Sarkin Rano, Ambasada Mohammad Isa Umar "Kwamishinan Harkokin Addini, na Kananan Hukumomi da Masarautu da na Ayyuka na Musamman da Harkokin Mata" Shugaban karamar hukumar Bunkure da sauran manyan jami'an gwamnati.