Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bankado wasu kura-kurai a tsarin biyan albashin ma’aikata, inda ta bayyana cewa ma’aikata 240 ne ke karbar albashi biyu.
Dakta Sulaiman Wali Sani, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin ma’aikata kuma shugaban kwamitin gudanarwa na jiha da aka dorawa alhakin tsaftace albashin gwamnatin jihar, ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai a nan Kano.
Dakta Sani, wanda ya wakilci sakataren gwamnatin jihar (SSG) a yayin taron, ya ce wannan bincike na daga cikin kokarin da ake yi na tsaftace ma’aikatan jihar.
Kazali ka Ya ce binciken ya biyo bayan wani aikin tantance ma’aikata da kuma ayyukan kwamitoci guda biyu - daya kan batun biyan albashin kananan hukumomi da aka kafa domin tantance tsarin albashi.
Ya kara da cewa ma’aikata 1,335 su ma sun kasa kawo bayanai domin tantancewa sama da watanni shida, lamarin da ya kara nuna damuwa kan sahihancin sunayen da yawa a cikin albashin gwamnati.