Mai girma Amb. Bello Sani Maitakalma,
Sa'in Hausawan Afrika,
Jarumin Arewa, Garkuwar Sarkin Malaman Abuja, Shugaban rukunin kamfanin Maitakalma global travels ya taya al'ummar muslumi murnar barka da Karamar sallah.
"Muna taya al'ummar jihar Kano da Arewacin Najeriya murnar Barka da karamar Sallah, muna kuma kira ga matasa da a zauna lafiya a guji kirƙiro da duk wani yanayi da zai kawo fitina a cikin al'umma.
Bamu da inda ya wuce wannan jiha da kasa bakidaya, Kano da Najeriya isune madubin kasashen africa, muzama masu dattako da kaunar junan mu, da rokon Ubangiji ya cigaba da azurta Kano kasa baki daya da dauwamamen zaman lafiya, arziki, kaunar junan mu" A cewar sa.
Ya kara da cewar "Ina kara amfani da wannan dama domin nayi kira ga al'umma wajen sanya shugabanninmu cikin addu'a, ubangiji ya basu ikon aika daidai, ya hanesu aikata akasin hakan.
Allah ya maimaita mana."