Na daina yiwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf adawa - Dan Bilki Kwamandan
Na daina yiwa Abba Kabir Yusif Adawa har sai in na kasa isar da sakon gyara gareshi to wajibi ne mu sanar dashi ta gidajen radiyo, domin zuciyarsa tana kan talakawan jahar Kano”
Abdulmajeed Dan Bilki Kwamanda ya bayyana hakan ne cikin wani sako daya wallafa a shafinsa.
Inda yace “Idan kaga na sake yiwa Engr. Abba Kabir Yusuf Adawa sai in na kasa isar da sakon a gyara gareshi to wajibine mu sanar dashi ta gidan Radio”.
Dan Binki Kwamanda na cikin mutanen da a baya sukai kaurin suna wajan sukar tsarin Kwankwasiyya a siyasance.