NDLEA ta kai samame a mafakar ƴan shaye-shaye a Kano tare da kama mutane 22
Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta ce ta kama mutane 22 da ake zargi da laifukan da suka shafi ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.
A cikin wata sanarwa da Sadiq Muhammad-Maigatari, mai magana da yawun hukumar a Kano ya fitar, hukumar ta bayyana cewa kamen ya biyo bayan jerin samamen da aka tsara a wurare da dama.
Ya ce wannan aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin kwamandan NDLEA na jihar Kano, Abubakar Idris-Ahmad, na ƙara zafafa yaki da safarar miyagun ƙwayoyi da amfani da su.
"A ranar 10 ga Afrilu, hukumar ta kawar da wasu maboyar miyagun ƙwayoyi da ke wajen ginin Dan’agundi, yankin Gwangwazo, Farm Center da ke kan hanyar Zaria, Tashar Rami da kuma Filin Idi a Kano," in ji shi.
"Wannan samame yana nuna jajircewar rundunar wajen ci gaba da yaki da safarar da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi, wanda ke zama barazana ga tsaron jama’a da lafiyar al’umma."
Mai magana da yawun hukumar ya ce jami’an NDLEA sun kwato nau’ikan miyagun ƙwayoyi yayin samamen.