Rundunar Yan sandan ta kasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Wannan umarni ya fito ne ta bakin mai magana da yawun ‘yan sanda na Æ™asa, Olumuyiwa Adejobi, bayan shigar wasu masu ruwa da tsaki na Æ™asar nan cikin al’amarin.
Sufeto Janar na ‘yansandan ya kuma umurci rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ta karÉ“i bayanin sarki Muhammad Sanusi a jihar dangane da abin da ya faru.
Egbetokun ya jaddada cewa janye matakin da aka É—auka tun da farko yana da alaÆ™a da kudirin rundunar ‘yan sanda na tabbatar da adalci tare da guje wa siyasantar da ayyukan ‘yan sanda ko fassararsu da wata manufa ta daban.