Saudiyya ta gargaɗi maniyyata kan zuwa aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta gargadi maniyyata aikin Hajji, kan su kula da kamfanonin tafiye-tafiye na biyu da kuma shiga kasar ta ɓarauniyar hanya.
Ma'aikatar ta kuma jaddada cewa duk wani bayani ko tayi da aka bayar ta hanyoyin da ba na hukuma ba, yaudara ce kuma ba ta wakiltar ma'aikatar ko wasu hukumomin da abin ya shafa.
Ma’aikatar ta yi kira ga kowa da kowa da ya kasance mai gaskiya da kuma guje wa tallan karya ko kuma tallar aikin Hajji na jabu.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, wajibi ne alhazan su samu takardar bizar aikin Hajji daga hukumomin da abin ya shafa a Masarautar, kuma hakan yana aiki ne da hadin gwiwar ofisoshin harkokin Hajji a kasashe 80, ko kuma ta hanyar “Nusuk Hajj” da aka kebe don mahajjata daga kasashe sama da 126. Ana samun yin ajiyar kai tsaye ta hanyar dandamali