Shelkwatar Ƴansanda Ƙasa ta gayyaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.
Tun da fari, rundunar ƴansanda tare da sauran hukumomin tsaro a jihar sun soke duk wani hawan sallah, musamman jerin gwanon dawaki a jihar, saboda dalilan tsaro.
Sai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallar idi a filin Idi na Kofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani dan banga da ke kare sarkin wuka har lahira, yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Bayan faruwar lamarin, wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa tun da farko babban sifeton yansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kama sarkin.
Sai dai kuma majiyoyin sun ce Kwamishinan ya bayyanawa Sufeto Janar din cewa, lamarin ba shi da alaka da kin yin hawan sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba kamar yadda al’adar ta tanada.
Watakila bai IGP bai gamsu da bayanin da Kwamishinan ya yi masa ba, sai ya umurci sashen binciken asiri na rundunar da ya gayyaci sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
A wata wasikar gayyata da ya sanya wa hannu, shugaban sashin, CP Olajide Ibitoye, ‘yan sandan sun gayyaci sarkin da ya gurfana a gaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar a ranar Talata 8 ga Afrilu da karfe 10 na safe.
Sai dai kuma wasu majiyoyi daga fadar Sarkin sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Sarkin bai samu takardar gayyatar a hukumance ba.