SHIN DAMAR KAWO ƘARSHEN RIKICIN MASARAUTAR KANO TA SAMU?
Ya kamata gwamnatin Kano ta yi amfani da wannan dama ta ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano Abbas Sanusi domin daidaita rikicin masarautar Kano. A dalilin wannan rasuwa, shugabanni sun haɗe kan su, sun nuna zumunci, sun yi wa juna addua, mu kuma talakawa kun bar mu muna gaba da zagin juna.
Wannan rikici ba wai wadanda ke taƙaddama akan sarautar kawai ya shafa ba, har jama’ar jihar Kano da kullum ake sa su cikin zulumi da fargaba. Wannan rikici yana daya daga abin da ya dawo da rikicin daba sosai a jihar Kano, kuma yake jawo asarar rayuka da dukiya.
Ba za mu fahimci dalilin rikicin ba, ba tare da dauko tushen rigimar ba. Babban dalilin da ya sa Aminu Babba Dan’Augundi ya samu saɓani da marigayi Sarkin Kano Ado Bayero shi ne goyon bayan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso (tun kafin a kirkiri kalmar “Kwankwasiyya”). Duk wani ɗan-takifen Kwankwaso, to sai dai ya biyo bayan Sarkin Dawaki.
Sarkin Dawaki ya ba da gudunmawa sosai a tafiyar Kwankwaso tun daga 1999 zuwa 2003, da kuma a shekarar 2011. A dalilin haka ya sa Ado Bayero ya tuɓe shi daga hakimci kuma ya karɓe masa ƙasa. Wannan ya sa Sarkin Dawaki ya kai marigayı Ado Bayero ƙara har kotun ƙoli.
A lokacin da aka naɗa Muhammadu Sanusi Sarki bayan rasuwar Sarki Ado Bayero a watan June, 2014, a cikin abubuwa uku da Kwankwaso ya nema sabon sarki zai yi bayan naɗa shi sarauta akwai dawo da Aminu Babba Dan’Agundi a matsayinsa na Sarkin Dawaki mai Tuta. Wannan ya na nuna alaƙar da ke tsakanin Kwankwaso da Aminu Babba.
Tabbas Sarki Sanusi bai biya wa Kwankwaso wannan bukata ba. Hujjar da Sarki Sanusi ya kawo ita ce, tun da maganar tana kotu a jira a gama shari’a zai bi abin da kotu ta umarce shi ya yi. Ya yi wa Kwankwaso bayanin cewa cire Bello Tuta wanda Ado Bayero ya maye gurbin Aminu Babba da shi zai kawo rikici tsakanin gidajen biyu. Sarki Sanusi ya ƙara da cewa, ko da Aminu Babba bai yi nasara a kotu ba, to zai iya neman wata sarautar, in kuma ba shi da ra’ayin yin sarautar ne, to zai kawo wani a yi masa.
A da can akwai zumunci tsakanin Sanusi da Aminu Babba Dan’Agundi, domin yana cikin wadanda su ka raka Sanusi tantace shi gaban majalisar dattawa kafin a nada shi makamın gwamnan bankin CBN. Haka-zalika shi ma Sanusi ya kyautata wa Aminu Babba Dan’Agundi lokacin da aka ɗaure shi a kurkuku bisa zargin kisan matar tsohon Gwamnan Kano Muhammadu Abubakar Rimi.
Bayan Kwankwaso ya bar mulki a 2015, Aminu Babba na cikin waɗanda Ganduje ya yi sauri ya ja a jika, watakil domin ya san Jangwarzo ne, kuma zai taya shi faɗa da Kwankwaso. Da Ganduje ya cire Sarki Sanusi ya nada Aminu Ado Bayero a watan March 2020, sai Ganduje ya sa aka mayar da Aminu Babba, aka canja fasalin sunan sarautar.
Na san da cewa Gwamna Abba ba shi da niyyar wulaƙanta zuri’ar Ado Bayero. Kafin Gwamna Abba cire Sarki Aminu, na san da cewa sai da ya gana da shugaban kasa, ya nemi sahalewarsa. A ganawar da su ka yi, ya tabbatar wa da shugaban ƙasa cewa har gida zai siya wa Sarki Aminu a Kaduna ko Abuja domin ya zauna cikin aminci.
Gwamnatin tarayya da jigajigan jam’iyyar APC ya kamata su sani cewa yanzu ba zamanin NEPU da NPC ake ba. Tsakanin sarakunan biyu, babu wanda zai iya canja ra’ayin al’ummar Kano ranar zabe. Ya kamata jigajigan APC su lura da cewa amfani da karfin iko na gwamnatin tarayya don cuzgunawa abokan hamayya zai iya jawo musu tausayi a idon jama’a; kuma abokan hamayya za su iya amfani da wannan gaɓa su gwara APC da jama’a cewa jam’iyyarsu ba ta kaunar walwalar jama’a shi ya sa ta hana hawan sallah bayan ta kawo ƙuncin rayuwa.
A zamanin mulkin mallaka ne sarakuna ke da tasirin sauya ra’ayin mutane. Wannan ya sa Maitama Danmasani na jam’iyyar NPC ya taɓa kayar da Mallam Aminu Kano na jam’iyyar NEPU a zaben majilisar tarayya na 1954. Haka zalika, tasirin masarauta ya sa Ahmadu Dantata shi ma ya kada Mallam a zaɓen shiyya na shekarar 1956.
Ya kamata gwamnatin jihar Kano ta nemi Sarkin Dawaki da ‘yayan marigayı Ado Bayero su daidaita, a daina jan kimar masarautar Kano a kwararo. Siyasar da ta sa Sarki Aminu ya cika burinsa na zama sarki, ita ta kawo karshen wa’adinsa na zama Sarki. A hakikanin gaskiya Sarki Aminu Ado Bayero ba shi da ƙara ko ɗaya a gaban kotu, haka zalika Sarki Sanusi babu wanda ya kai shi ƙara gaban kotu. Aminu Babba Dan Agundi ne ke ƙara, watakil saboda tunanin Sarki Sanusi ba zai bar masa sarautarsa ta Sarkin Dawaki Babba ba in ya zauna karagar mulki.
Ya kamata ku yi karatun ta-natsu, ku kawo ƙarshen zubar da kimar wannan masarauta da garin Kano. Ku nemi Aminu Baba Dan’Agundi da wasu manya a ‘yayan marigayi Ado Bayero ku zauna a samu maslaha. Sarki Sanusi ya bar Aminu Babba da sarautarsa (kai a kara wa gidansu wata sarautar ma); a dawo wa zuri’ar Ado Bayero sarautun su da Sarki Aminu Bayero ya nada su, kuma a giną wa Sarki Aminu gida mai kima a garin da yaka so.
Ku duba lamarin nan.