Jami'in hulÉ—a da jama'a na hukumar ta KAROTA, a Kano, Abubakar Ibrahim ShadaÉ—a, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Jaridar Raihana a ranar Alhamis.
Hukumar ta ce, daga cikin waÉ—anda ake zargi har da wani jami'in soja da direban motar da kuma yaron sa.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya ce a daren jiya Laraba ne jami'an Hukumar KAROTA, suka kama wani Direban motar fakas (Container) da ake zargin sa da sanadiyar rasa ran wani Jami'n Hukumar a jihar mai suna Yahaya Barista, a lokacin da yake gudanar da aikin sa.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan, bayan da hukumar ta KAROTA ta ce ba zata lamunci cin zarafin da al'umma ke yiwa jami'anta a yayin da suke tsaka da aiki ba.