YANZU-YANZU: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadiman Kano
Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya amince da Alhaji Mannir Sunusi Hakimin Bichi a matsayin sabon Galadiman Kano.
A ranar talatar data gabata ne Allah ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi rasuwa, wanda hakan ta ba da damar maye gurbin nasa.
Sabon Galadiman Alhaji Mannir Sanusi shi ne ya bayyana hakan ga wakilin kadaura24 a ranar talata .
Ya ce Sarki Sanusi II ya amince da nadin ne bayan da ya tattauna da masu ruwa da tsaki na Masarautar, inda daga karshe aka amince Alhaji Mannir Sanusi ya za ma sabon Galadiman Kano.
Mannir Sanusi ya kara da cewa Sarki ya kuma amince da nada Turakin Kano A Matsayin Sabon Wamban Kano, yayin da Adam Sanusi aka nada shi a matsayin Tafidan Kano.