Zamu Isar da Rahoton Gaggawa na Gobarar Fagge Ga Gwamnan Kano Domin Neman - Amb. (Dr) Maimuna Umar Sheriff
Daga Bashir A Bashir T/Wada
Amb. (Dr) Maimuna Umar Sheriff, mai ba wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin Community Policing, ta bayyana cewa za ta isar da rahoton gaggawa na gobarar da ta shafi Babban Ofishin ‘Yan Sanda na Fagge ga Gwamnan domin neman daukin Mai girma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Amb. Ta bayyana hakane a lokacin da ta ziyarar jaje ga Yan sandan Fagge, ta kuma ziyaraci Hakimin Fagge a fadar sa.
Gobarar, wadda ta tashi a Babban Ofishin ‘Yan Sanda da ke unguwar Fagge, ta haddasa asarar muhimman kayayyaki da dama, ciki har da babura masu kafa Biyu, takardu masu muhimmanci, da kuma lalacewar wasu kayayyakin aiki na jami’an tsaro.
Amb. Maimuna ta bayyana cewa, duk da gaggawar da ake bukata wajen farfado da ayyukan ofishin. Hakan zai samar da ci gaba da walwala ga al’ummar yankin tare da kuma tabbatar da lafiyar al’umma da kare dukiyoyinsu.
“Fagge cibiyar kasuwanci ce mai matukar muhimmanci, don haka samar da tsaro mai inganci a yankin zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da inganta harkokin kasuwanci,” a cewar ta
Amb. Dr Maimuna ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin zamanantar da ofishin ta hanyar sanya na'ura Mai kwakwalwa da kayan aikin zamani domin bunkasa ayyuka da kuma inganta adana bayanai yadda ya kamata.
Daga karshe ta jajantawa Rundunar Yan sandan Kano, bisa wannan iftila'i dama al'ummar karamar hukumar Fagge, da addu'ar Ubangiji ya kare faruwar hakan a nan gaba.